Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero



Mai Martaba Sarkin Bichi
Alhaji Aminu Ado Bayero
Hoto:  BBC Hausa


Gabatarwa

Mai Martaba Sakin Bichi na farko, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne ɗa na biyu a wajen Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Ado Bayero. Mutum ne mai matuƙar gogewa a harkar sarauta tare kuma da farin jini a wajen jama’ar Jahar Kano saboda kulawar sa da harkokin jama’a. Masanin aikin jarida da kuma gyaran jirgin sama. Cikin wannan rubutun za ku san yadda hakan ta wakana.

Haihuwa

An haifi Mai Martaba Sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero a Gidan Rumfa; Fadar Masarautar Kano a ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 1961.

Salsala

Alhaji Aminu Ado Bayero, zuriyar gidan malam Ibrahim Dabo ne ta ɓangaren Marigayi Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.

Shi ɗa ne ga Alhaji Ado Bayero, sarkin kano na goma sha uku a cikin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Alhaji Abdullahi Bayero, sarkin Kano na goma a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Sarkin Kano Muhammadu Abbas, sarki na tara a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Abdullahi Maje Karofi, sarkin Kano na uku a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Malam Ibrahim Dabo, sarki na biyu a cikin jerin sarakunan Fulani sannan kuma ɗaya daga cikin mayaƙan Shehu Usmanu Ɗanfodiye waɗanda suka kawo tutar jihadi zuwa Kano tare da kafa daular Musulunci a masarautar Kano.

Haka nan ta ɓangaren mahaifiyarsa, Mai Martaba Sarkin Bichi ɗa ne ga Hajiya… wadda ita kuma ‘ya ce ga Mai Martaba Sakin Ilorin, Alhaji Sulu Gambari…

Karatu

Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi karatunsa na firmare a Makarantar Fimare ta Ƙofar Kudu wanda bayan ya kammala kuma ya samu Nasarar shiga Kwalejin Gwamnati da ke Birnin Kudu. Daga nan kuma ya shiga Jami’ar Bayero da ke Kano ya samu digiri a fannin aikin jarida.

Daga baya ya samu zuwa Makarantar Koyon Tuƙin Jirgin Sama da ke Ƙasar Amurka (Flying College, Oakland, California, US), Maduagwu, (2020).

Gagayyar Aiki

Shafin Wikipedia (2020), ya ruwaito cewa, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi aiki da kamfanin sufurin jiragen sama na Kabo Air da farko a matsayin jami’in hulɗa da jama’a, daga baya kuma injiniyan jirgi.

Gogayyar Sarauta

  • Ɗanmajen Kano, Hakimin Dala, 1990.
  • Ɗanburan, Hakimin Dala, 1990.
  • Turakin Kano, Hakimin Dala, 1992.
  • Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala, 2000.
  • Wamban Kano, Hakimin Dala. 2014.

Maruwaita, Maduagwu, (2020) da kuma Adewale, (2019).

Sarkin Bichi

Bayan taka muƙaman sarauta ɗaya-bayan-ɗaya, Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu nasarar zamowa sarkin Bichi na farko. Naɗin da aka yi masa a ranar Juma’a a cikin shekarar 2019.

Jawabin Sarkin Bichi

A wata tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi da wakinlin jaridar The Guardian, Murtala Adewale sannan kuma aka wallafa a shafin Internet na jaridar, Sarkin ya bayyana cewa: “Bari na faɗi cewa, Allah ne mai bayar da mulki da muƙami kuma cikin ikonSa da ƙarfin mulkinSa, Yake bayar da mulki da muƙami ga duk wanda Ya so. Yanzu bari na gaya muku wannan sirrin, tun a karon farko da aka yi min naɗin sarauta bisa al’ada har zuwa wannan lokacin da aka naɗa ni a matsayin Sarkin Bichi, ban taɓa ba, kuma bari na sake maimaitawa, ban taɓa zuwa wajen wani mutum na ce da shi don Allah bani wannan muƙamin ba. Bana roƙon muƙami; na yi imani cewa dukkan abin da ya zo gare ni daga Allah yake”.

Manazarta:


Adewale M. (2019). ‘The split of Kano Emirate was neɓer my wish, but things change with time’. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://guardian.ng/saturday-magazine/the-split-of-kano-emirate-was-neɓer-my-wish-but-things-change-with-time.

BBC Hausa (2019). An bai wa Aminu Ado Bayero sarautar Bichi. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.bbc.com/hausa/labarai-48232909.

Maduagwu C. (2020). Brief Biography Of The New Emir Of Kano, Aminu Ado Bayero. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.neɗtedition.com.ng/brief-biography-of-the-new-emir-of-kano-aminu-ado-bayero.

Nasir J. (2020). Profile: Ado Bayero, the mass communication graduate who ‘neɓer begged’ for titles. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.thecable.ng/profile-ado-bayero-the-mass-communication-graduate-who-neɓer-begged-for-titles.

Wikipedia (2020). Aminu Ado Bayero. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Aminu_Ado_Bayero

Sarakuna


Kasuwanni


Bukukuwa


Wasu Gurare


Yaƙuƙuwa


Ƙofofin Bichi


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub